Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hong Lei ya sanar da cewa, a kwanan baya, bangaren Austria ya kyale suka da bangaren Sin ya yi masa har sau da dama, ya shirya irin wannan ganawa tsakanin shugaban gwamnatinsa. Sakamakon haka, wannan lamari mai fuskoki da yawa ke tsoma baki kan karkokin cikin gidan kasar Sin, kuma ya bakantama 'yan kasar Sin rayuka, da kawo wasu alamu na rashin gaskiya ga 'yan gwagwarmayar kawo barakar yankin Tibet mai cin gashin kanshi daga kasar Sin.
Ya sanar da cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a Beijing da jakadan kasar Sin dake kasar Austria, su ne wakilan kasar Sin a bangaren Austria. Maganar yankin Tibet batun cikin gida ne kawai na kasar Sin. Dalai Lama ya kasance dan gudun hijirar siyasa dake cikin gudanar da aiyukan tada zaune tsaye ga kasar Sin da sunan addini, cewar Hong. Kasar Sin ba ta goyi bayan saduwa tsakanin hukumomin kasashen waje tare da Dalai Lama ta ko wani fanni, da ko wace kasa da kuma kowa, kuma ba ta goyi bayan lamuren shiga cikin harkokin gidanta ta hanyar yin amfani da Dalai.
Hong ya jawo hankalin kasar Austria da ta dauki matsayin kasar Sin da muhimmanci da kuma dakatar da goyon bayan masu adawa da kasar Sin 'yan gwagwormayar kawo barakar yankin Tibet mai cin gashin kai daga kasar Sin, tare da gaugauta daukar matakan da suka dace wajen kawar da irin wadannan lamura, domin kare tafiyar da ci gaban hulda tsakanin kasashen guda biyu. (Abdou Halilou)