Kasar Sin ta ce, Amurka ta bijirewa rashin jin dadin da Sin ta nuna, har ma shugabanta Barack Obama ya gana da Dalai a fadar White House, al'amarin da ya kasance katsalandan cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, da kawo illa ga babbar moriyar kasar Sin da huldar dake tsakaninta da kasar Amurka. Kasar Sin ta nuna matukar takaici da adawa da wannan batu.
Bugu da kari kuma, kasar Sin ta jaddada cewa, Tibet wani yanki ne da ba'a iya raba shi daga kasar Sin, harkokin yankin harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna yin tsayin daka wajen kiyaye babbar moriyar kasar da mutuncin al'ummarta.
A wata sabuwa kuma, da sanyin-safiyar wannan rana, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Ma Zhaoxu ya yi jawabin cewa, Dalai ya dade yana tafiyar da ayyukan kawowa kasar Sin baraka ta hanyar fakewa da addini, gaskiyar maganar ita ce shi dan gudun-hijira ne. Kasar Sin tana tsayawa haikan wajen kin yarda da duk wata ganawa da aka yi tsakanin shugaban wata kasa da Dalai, haka kuma tana kin amincewa da kutsa kai da duk wata kasa ko wani mutum ya yi cikin harkokin cikin gida na kasar Sin ta hanyar ganawa da Dalai. Abun da kasar Amurka ta yi, wato amincewa da ziyarar Dalai a kasar har ma da shirya ganawa tsakaninsa da shugaban kasar, ya sabawa babbar ka'idar dangantakar kasa da kasa da alkawarin da gwamnatin Amurka ta dauka. Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta mutunta matsayin da Sin ta dauka, da daukar matakai ba tare da bata lokaci ba don rage mummunan tasiri da wannan lamari ya haifar, da daina yin katsalandan cikin harkokin gida na Sin, da dakatar da nuna goyon-baya ga mutanen dake neman 'yancin kan Tibetta hanyar da ta sabawa ka'idar kasar Sin.(Murtala)