Shugaban hukumar addinin Musulunci ta kasar Sin, kuma babban limami Chen Guangyuan wanda ya yi jawabin a gun bikin, tare da taya murna ga 'yan uwa musulmi dake kasar Sin da ma duk fadin duniya, ya ce, a lokacin bikin babbar sallah, ana fatan alheri ga addinin Musulunci da ya habaka a nan kasar Sin a karkashin jagorancin JKS,
Ya kuma nuna fatan kasar Sin za ta bunkasa lami lafiya, jama'ar kasar su ma za su ji dadin zaman rayuwa, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.(Fatima)