in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An damke mashiryin fim din yin batanci ga Musulunci bisa zargin karya ka'idar kotu
2012-09-28 11:53:39 cri

Yan sanda a birnin Los Angeles na kasar Amurka sun cafke Nakoula Basseley Nakoula, mashiryin fim din nan da ya yi batanci ga addinin Musulunci a Alhamis din nan, sakamakon zargin karya ka'idar da kotu ta gindaya masa, wadda ta haramta masa amfani da yanar gizo, ko wakilta wani ya yi amfani da ita a madadin sa, ba tare da tuntubar jami'in dake lura da shi ba.

An rawaito wata kafar yada labaru a birnin na Los Angeles na cewa, Nakoula, dan shekaru 55 da haihuwa, wanda kuma ke amsa sunan Sam Bacile dake zaune a garin Cerritos, a California, ya taba shafe watanni 21 a gidan kaso, ya kuma biya diyyar dalar Amurka sama da dubu 790 cikin shekarar 2010, sakamakon hukuncin da wata kotu ta yanke masa, kan laifin sata, da yin sojan-gona, tare da damfarar wani banki. Haka zalika kotun ta bukace shi da ya zamo karkashin haramcin amfani da yanar gizo cikin shekaru 5, har sai ya nemi izini, bayan kammala wa'adin sa a gidan kaso cikin shekarar 2011.

Jaridar ta "The Los Angeles Times", ta kara da cewa, Nakoula, na iya fuskantar tuhuma sakamakon karya wancan sharadi na kotu, duk dai da cewa, an gabatar da takardun cafke Nakoula ga kotun cikin shiri. Bugu da kari, rahotanni na nuna cewa, Nakoula zai bayyana gaban wata kotu dake birnin Los Angeles a yammacin Alhamis din nan.

Shi dai wannan fim da Nakoula ya jagoranci shiryawa, wanda kuma aka kebewa dalar Amurka dubu 250, ya tunzura dimbin musulmai da ke sassan duniya, shiga zanga-zangar nuna bacin ransu ga cin zarafin Musulunci da fim din ke kunshe da shi, bayan da aka fidda wani yankinsa a shafin yanar gizo na "You tube". Wannan dai zanga-zanga ta yadu a kasashe da dama ciki har da Masar, da Yemen da kuma kasar Libya, inda tsanantar boren ya haddasa kisan jakadan Amurka Chris Stevens, tare da wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Amurkan su uku.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China