"dukkan wasu matakan ladabtarwa da hukuntawa dake cikin dokar kasa da za su taimakawa wajen ganin duk wasu masu kawo tashin hankali cikin kasa sun dandana wukar kudarsu, kuma wadanda suka aikata kisa su ma kisa zai hau kansu" in ji shugaba Jammeh.
Haka kuma ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta ba da dama ga 'yan ta'adda ko masu fashi da makami su ci gaba da addabar kashi 99 cikin 100 na al'ummar kasar ba.
Shugaba Yahya Jammeh yayi wadannan kalamai a lokacin da ayyukan ta'addanci da kashe kashe, tare mutane ke kan hanya, sace sace da garkuwa da mutane suka yi kamari a cikin kasar.
"Burinmu shi ne kafa wata kasar zaman lafiya da jituwa da babu tashe tashen hankali", in ji shugaban kasar Gambia tare da daukar niyyar karfafa matakan tsaro da na shari'a domin daidaita wannan matsala. (Maman Ada)