in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban majalisar NPC ta kasar Sin a Uganda
2013-09-18 17:35:22 cri


Bisa goron gayyatar da shugabar majalisar dokokin kasar Uganda Rebecca Alitwala Kadaga ta yi mata, shugaban majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Zhang Dejiang ya kai ziyarar sada zumunta a kasar daga ranar 16 zuwa ranar 17 ga wata, inda a birnin Entebbe na kasar, Mista Zhang ya gana da shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni, kana a birnin Kampala, ya gana da firaministan kasar Amama Mbabazi, tare da yin shawarwari da takwararsa ta kasar, madam Alitwala Kadaga.

Yayin da Mr.Zhang Dejiang, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke ganawa da Shugaban kasar Uganda Museveni, Mista Zhang ya isar da sakon gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping gare shi. Yana mai cewa, shugaba Museveni ya tabbatar da mu'amala tare da shugabannin kasar Sin na da da na yanzu cikin wani dogon lokaci, kuma ya ba da babbar gudummawa wajen raya dangantar dake tsakanin kasashen biyu. Bayan da kasashen Sin da Uganda suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu yau da shekaru 51 da suka gabata, bangarorin biyu sun rike fa'idar girmama juna bisa tushen zama tare cikin daidaito, sada zumunta da amincewa da juna, kuma kasashen biyu sun tabbatar da tuntubar juna tsakanin gwamnatoci da majalisun dokoki, jam'iyyun siyasa da kananan hukumomi nasu, kuma hadin gwiwar da ke tsakaninsu na bunkasa a fannoni daban daban. Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Uganda sun yi shawarwari a gun taron shugabannin kasashen BRICS da aka yi a kasar Afrika ta Kudu, da suka samar da sakamako mai gamsarwa, kuma a wannan ziyarata, zan yi kokarin tabbatar da daidaiton da shugabannin suka cimma a yayin taron, da kara inganta dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, tare da sa kaimin hadin gwiwa daga dukkan fannoni a tsakaninsu, don samar da kuzari ga bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasar Uganda wajen lalubo bakin zaren samun bunkasuwa bisa yin la'akari da halin da kasar take ciki.

Zhang Dejiang ya ci gaba da cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya zama babbar manufar diplomasiyya da kasar Sin take bi, kana kuma, ginshikin manyan tsare-tsare da kasar Sin za ta nace wa kansu cikin dogon lokaci. Yanzu al'ummar kasar Sin na dukufa ka'in da na'in wajen cimma burin farfado da kasar. Burin da kasar Sin ke neman cimmawa shi ne samun wadatar kasa, da farfado da al'ummarta, da kawo alheri ga jama'a, haka kuma shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a duniya. Kasar Sin na fatan hada kanta da kasashen Afrika, don cimma burinsu da samun bunkasuwa.

A nasa bangare kuma, Museveni ya mika gaisuwa da fatan alheri ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping. Yana mai cewa, kasar Sin babbar kawa ce ga Uganda, kasar Uganda tana nuna godiya ga goyon baya da taimako da kasar Sin take ba ta cikin dogon lokaci. Ya ce, yanzu, kasashen Afrika na cikin wani muhimmin lokaci na samun ci gabansu, don haka, Sin da kasashen Afirka na fuskantar damar karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Ya yi imani kan cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, dangantakar da ke tsakanin kasashen Uganda da Sin da ma dangantakar dake tsakanin kasashen Afrika da Sin za ta samu makoma mai haske.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China