in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron MDD ya zartas da yarjejeniyar cinikayyar makamai
2013-04-03 12:55:43 cri

Ran 2 ga wata da safe ne aka kira cikakken taro na babban zaman MDD karo na 67, inda aka zartas da yarjejeniyar cinikayyar makamai, don sa ido kan harkokin cinikayyar makaman yaki tsakanin kasashen duniya.

Wannan yarjejeniyar cinikayyar makamai ita ce yarjejeniya ta farko, ta duk duniya, wadda za ta ba da damar sa ido kan harkokin cinikayyar makaman yaki. A halin yanzu, yawan kudaden da ake kashewa wajen cinikayyar makamai ya haura dallar Amurka biliyan dari cikin ko wace shekara. Yarjejeniyar dai za ta lura da harkokin cinikayyar makamai da za su shafi kudi, da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan saba'in a dukkanin fadin duniya.

An zartas da yarjejeniyar tare da samun kuri'un amincewa 154, da kuri'un nuna adawa guda 3, tare da kuma na wadanda ba su jefa kuri'a ba guda 23. Cikin kuma wannan adadi, kasashen Koriya ta Arewa, da Iran, da Syria sun jefa kuri'un nuna adawa da yarjejeniyar, yayin da kasashen Rasha, da India, da Sin, da dai sauransu ba su jefa kuri'a ba.

Bayan zaman jefa kuri'ar, mataimakin zaunannen wakilin Sin da ke MDD Wang Min, ya jadadda cewa, kasar Sin ba ta yarda da yadda aka zartas da yarjejeniyar kayyade makamai, da ta shafi yanayin tsaron kasa da kasa ta hanyar amfani da karfin iko, kuma tana damuwa kan cewa abin zai zama mugun misali ga shawarwarin kayyade makamai na gaba . (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China