in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya bukaci da a yi taron koli na kungiyar OIC a kasar Saudiyya
2011-06-07 09:53:22 cri

Ranar Litinin 6 ga wata, shugaban karba-karba na kungiyar taron musulmai (OIC) kuma shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya nuna cewa, saboda halin da kasar Masar ke ciki ya kara tsananta, ya kamata a mayar da taron kolin OIC zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya wanda aka shirya yin shi a wannan shekara a Alkahira babban birnin kasar Masar.

A wannan rana a gun bikin bude taron masanan addinin Musulunci na kasa da kasa, Wade ya ce, ba za a iya tabbatar da yiwuwar lafiyar taron ba idan za a yi shi a kasar Masar. Idan wata kasa tana fuskantar rikici, bai kamata ta kira wani taron kasa da kasa ba. Hakan ya sa, ya yi kira da a canja wurin yin taron zuwa kasar Saudiyya.

An ba da labari cewa, wannan taron masana mai tsawon kwanaki 3 mai taken "Amfani da matsayin masanan addinin Musulunci karkashin sauyin duniya". Wakilai daga kasashe da yankuna 84 suke halarta.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China