in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya ki amincewa da fim dake batanci ga manzon Allah Annabi Muhammad (SAW)
2012-09-23 17:30:01 cri
A ranar 22 ga wata, kakakin shugaban kasar Masar Yasser Ali ya bayyana wa 'yan jarida cewa, shugaban kasar Masar Mohamed Morsy ya samu wata wasika daga shugaban kasar Amurka Barack Obama, inda Obama ya ki amincewa da fim dake batanci ga manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), wanda ya haddasa bazuwar nuna kiyayya ga Amurka a kasashe da dama, kana ya jaddada cewa, duk wani harin da aka kaiwa wadanda ba su da nasaba da lamarin ya zama laifi.

Ali ya ce, shugaba Obama ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Masar domin ta dauki matakan tabbatar da tsaron ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar, kana ya nuna yabo ga sanarwar da shugaba Morsy ya gabatar bayan da jama'ar kasar Masar suka yi zanga-zanga. Obama ya bayyana cewa, wannan sanarwa ta bayyana ra'ayin kasar Masar, wadda ta inganta dangantakar dake tsakanin kasar Masar da ta Amurka, kuma yana fatan zai yi kokari tare da shugaba Morsy wajen ci gaba da raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China