in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afrika za su cimma takardar visa guda ta yawon bude ido
2013-08-29 10:21:29 cri

Shugabannin kasashen gamayyar gabashin Afrika (EAC) sun cimma matsaya guda a ranar Laraba kan takarar visa ta yawon bude ido, da zummar bunkasa sana'ar yawon shakatawa da bude ido, bayan wata ganawarsu ta yini guda a birnin Mombasa na kasar Kenya. Ministocin kasashen Kenya, Uganda, Ruwanda, Sudan da kuma Burundi za su cimma kudurorin yin amfani da katin 'dan kasa a matsayin wasu takardu na yin tafiye-tafiye kafin ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2013. A yayin da yake jawabi a wannan dandali na EAC kan gine-ginen more rayuwar jama'a, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya nuna cewa, hukumomin kwastan da wadannan kasashe biyar na kokarin cimma wani tsarin yin shawagi cikin walwala na jama'a a cikin shiyyar EAC a cikin watan Janairun shekarar 2014. 'Mun samu cigaba da dama kan wannan magana ta takardar visa guda ta yawon bude ido da kuma baiwa jama'a damar amfani da katin 'dan kasa guda, katin zabe, da katin dalibai, ta yadda mutanenmu za su yawo cikin walwala a cikin kasashenmu.' in ji shugaba Uhuru Kenyatta. A cewar masu kula da harkokin sana'ar yawon bude ido, takardar visa guda za ta taimaka wajen warware wasu matsalolin tafiye-tafiye ga mutanen dake fatan zuwa wuraren shakatawa da bude ido a gabashin Afrika.

Kasashen EAC na kokarin cimma fasfo da takardar visa guda tun wajen shekarar 2005, a yayin da tabbatar da wannan buri da ke fuskantar kalubalolin tsaro, rashin gine-ginen more rayuwar jama'a da na daidaito kan matsayin aikin takardar visa da kuma yadda za'a raba kudaden shiga. A cewar shugaban kasar Kenya, albarkatun da ake da su na janyo hankalin masu zuba jari da kuma kasancewa wata kasuwa ta mutane fiye da miliyan 200. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China