in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi rantsuwar kaman aiki
2013-08-23 17:12:39 cri

A shekarar 2008, an samu rikici sakamakon babban zaben kasar Zimbabwe, bayan da gwamnatin hadaka ta shafe shekaru sama da 4 tana mulkin kasar, yanayin siyasa a kasar Zimbabwe ya samu kyautatuwa, kuma tattalin arzikin kasar ya samu farfadowa, amma kasashen Turai da Amurka ba su kawar da takunkumin da suka saka wa Zimbabwe ba, kuma akwai sauran rina a kaba wajen raya sana'ar masana'antu da aikin gona, kana an samu koma baya wajen raya muhimmman ababen more rayuwa, Mugabe da jam'iyyarsa za su yi kokari don tinkarar wadannan matsaloli. Yayin da Mugabe ke yakin neman zabe, Mugabe ya yi alkawarin cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, zai dauki matakai ciki har da raya sana'ar hakar ma'adinai, don samar da guraben aikin yi da yawansu zai kai sama da miliyan 2 a kasar, kuma zai yi hobbasa don tabbatar da matsaikacin yawan saurin karuwar tattalin arzikin kasar zuwa kashi 9 cikin 100. A cikin jawabin da ya yi, Mugabe ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi kokari don gina kasar, ya ce, "Ban da wasu kasashen yammacin duniya, ana ganin cewa, mun shirya babban zabe cikin zaman lafiya, da adalci kuma a bayyane, yau ba ma kawai ta kasance bikin rantsuwar kaman aikina ba, haka kuma ya nuna cewa, Zimbabwe za ta bude wani sabon shafi wajen samun ci gaba. Muna son yin amfani da wannan dama, don raya albarkatun da muke da su, don kawo alheri ga kasarmu."(Bako)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China