Robert Mugabe mai shekaru 89, wanda ya fi dadewa a dandalin siyasa na Afrika. Tun bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kai a shekarar 1980, Mugabe ya fara mulkin kasar har zuwa yanzu, shi ne shugaban kasa mafi shekaru a nahiyar. A babban zaben da aka yi a ranar 31 ga watan Yuli, jam'iyyar ZANU-PF da ke karkashin shugabancinsa ta samu gaggarumin rinjaye.
Sabo da kwarjininsa, shugabannin kasashen duniya da dama sun halarci bikin rantsuwar kama aikinsa, cikinsu har da shugabannin kasashen Namibiya, Tanzaniya, Mozambique, Kongo(kinshasa) da sauransu, haka kuma shugaban kasar Namibiya na farko Nujoma da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki da wasu tsaffin masanan siyasa na Afrika sun halarci bikin. A matsayinsa na manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin Li Liguo ya halarci bikin. Ya fada wa wakilinmu cewa, gwamnatin Sin za ta ci gaba da samar da taimako ga kasar Zimbabwe, kuma tana fatan karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a tsakaninsu. Yana mai cewa, "A madadin shugaban kasar Sin Xi Jinping da gwamnatin Sin, ina son bayyana cewa, yayin da za a raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu wato kasashen Sin da Zimbabwe a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da samar da taimako ta hanyoyi da dama ga Zimbabwe, kuma za ta sa kaimi ga masana'antun Sin da su je Zimbabwe don saka jari don samun nasara da moriyar juna tare."