Janyewar rukunin sojojin wanzar da zaman lafiya da bada taimako ga farfado da bangaren tsaro a kasar Guinee-Bissau (MISSANG), da aka tsaida ranar Laraba, ga dukkan alamu, an gusa wannan lokaci a cewar wata majiya mai tushe ta kusa da rundunar sojojin kasar Guinea-Bissau.
Tawagar MISSANG, dake kunshe da kusan mutane 600, za ta ci gaba da tsayawa har wasu 'yan kwanaki ko ma wasu 'yan makonni in ji wani jami'in rundunar sojojin kasar Guinea-Bissau, da ya bukaci sakaya sunansa. Babu wata ranar da aka tsaida duk da cewa, kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta bayyana a makon da ya gabata cewa, janyewar za ta fara wannan Laraba kuma za ta kwashe tsawon kwanaki hudu ko biyar.
"Jirgin ruwan da zai yi jigilar wadannan sojoji da kuma kayayyakinmu har yanzu bai iso Luwanda ba, domin haka muke jira." in ji wani hafsan sojojin Angola. (Maman Ada)