MDD a jiya Litinin 22 ga wata ta yi kakkausar suka ga harin da aka kai kan sansanin jiragen saman kasar Guinea-Bissau a ranar Lahadi tare da yin kira a kan bangarorin da abin ya shafa dake yammacin Afirka da su warware takaddamarsu cikin lumana.
Kakakin majalisar Martin Nesirky a cikin wata sanarwa ga manema labarai ya ce, "MDD ta soki wannan hari da kakkausar murya kuma mun ji takaici game da rayukan da suka salwanta a sanadiyyar wannan harin." Ya kara da cewa, "Muna bin sahun wannan al'amari sannu a hankali."
Mutane shida ne dai suka rasu rayukansu a wannan hari a sansanin jiragen sama na Bissalanca, mai tazaran kilomita 7 daga babban birnin kasar Bissau kamar yadda rahotanni suka bayar.
Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Guinea-Bissau a wata sanarwa daga baya ta ce, harin da aka kai wani yunkuri ne na son dawowa da hambaren firaministan kasar Carlos Gomes Junior "a bakin rayukan jama'a".
Carlos Gomes dai an tsare shi ne a ranar 12 ga watan Afrilu yayin wata juyin mulkin da sojoji suka yi, sannan suka sake shi ya tafi kasar kwaddibuwa a karshen watan.
Wakilin babban magatakardar MDD na musamman kuma shugaban ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD a Guinea-Bissau, Joseph Mutaboba yana cigaba da tuntuba da hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa dake Guinea-Bissau, kuma yana sanar da hedkwatar MDD da duk wani cigaban da ake samu, in ji sanarwar.(Fatimah)