Baya ga kokarin gwamnatoci da sauran kungiyoyi masu zaman kansu wajen taimakawa matasa ko dalibai a harkokinsu na karatu, su ma dalibai suna kokari a yayin da suke dogon hutu, inda suke kokarin neman aikin wucin-gadi don samun karin kudaden shiga.
Sai dai, a wasu lokutan irin wadannan dalibai kan fada hannun bata-gari da ke zaluntarsu da sunan samar masu aikin wucin-gadi yayin da suke dogon hutu.