in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada Phumzile Miambo-Ngcuka a matsayin jagorar hukumar kare hakkokin mata ta MDD
2013-07-11 10:44:34 cri

Rahotanni daga helkwatar MDD na bayyana cewa, magatakardar majalissar Ban Ki-Moon, ya amince da nadin tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Afirka ta Kudu, uwar gida Phumzile Miambo-Ngcuka, a matsayin shugabar hukuma mai lura da batun kare hakkokin mata ta MDD.

Miambo-Ngcuka, 'yar shekaru 57 da haihuwa, kuma mace ta farko da ta taba rike mukamin mataimakiyar shugaban kasa a Afirka ta Kudun, ta maye gurbin Michelle Bachelet, tsohuwar shugaban kasar Chile da a yanzu haka ke burin sake tsayawa takarar kujerar shugabancin kasarta a karo na biyu. Sanarwar nadin uwar gida Miambo-Ngcuka a matsayin jagorar wannan hukuma ta kare hakkokin mata, na kunshe da kyakkyawan fatan cewa, sabuwar jagorar za ta yi amfani da dinbin kwarewarta, wajen bunkasa ayyukan kyautata rayuwar mata.

Kafin rikon mukamin mataimakiyar shugaban kasar Afrika ta Kudu tsakanin shekarun 2005 zuwa 2008, Miambo-Ngcuka ta taba rike mukamin mataimakiyar ministar ciniki da masana'antu, da mukamin minista a ma'aikatar ma'adanai da makamashi, da kuma mukamin minista a ma'aikatar al'adu, kimiyyar da fasaha. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China