in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Gabon sun sanya hannu kan kwangila domin gyara tashar ruwan Port-Mole dake Libreville
2013-06-17 10:41:23 cri

Kamfanin manyan gine-gine (ANGT) na kasar Gabon da kamfanin 'Harbour Engenering' na kasar Sin sun rattaba hannu kwanan nan kan kwangilar dalar Amurka miliyan 120 domin gyara tashar ruwan Port-Mole dake Libreville, babban birnin kasar Gabon, kwanan baya a yayin taron New York kan Afrika (NYFA) karo na biyu, da ya kasance dandalin bunkasa zuba jarin kasashen waje a Afrika da ke gudanarwa tun daga bakin shekarar 2012 a Libreville.

Zangon farko na wannan aiki ya shafi sake gyara tsohuwar tashar ruwan Libreville domin zama wani wurin cigaban fasahar zamani, da gwamnatin kasar Gabon ta dauki niyyar zuba jarin dalar Amurka miliyan 4 da dubu 500, wanda bisa fadin kadada 45, za'a gina cibiyar shirya taruruka mai daukar mutane 7500 zuwa 10000, gidan kallo, shaguna, gidajen otel, da sauransu. Tashar ruwan Port-Mole ta yanzu na karbar jiragen ruwan kamun kifi ko na yawon bude ido da kuma jiragen manyan mutanen kasar Gabon bisa fadin kadada 4, bayan da aka gyara ta, za ta iyar karbar wasu jiragen ruwa da za su fito daga sauran kasashe, musammun ma daga kasar Kamaru. Kana zango na biyu na kwangilar dake cikin tsarin gwamnati na cigaban gine-gine a dukkan fadin kasar ya shafi dalar Amurka biliyan 20 bisa wa'adin shekarar 2012 zuwa 2016, kuma babban burin wadannan ayyuka shi ne na daukaka sunan kasar Gabon a duniya da kuma gyara mahadar Boulevard Triomphal, wata babbar hanyar dake Libreville. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Shugaban wucin gadin CAR ya isa Gabon 2013-05-16 10:44:03
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China