Mr. Zuma ya ce, yawan nakasassun da suke zaune a duk duniya ya kai kimanin miliyan 650, wato ya kai kashi 10 cikin kashi dari bisa na jimillar mutanen duk duniya, kuma kashi 80 cikin kashi dari daga cikinsu suna zaune a kasashe masu tasowa. A cikin 'yan shekarun nan, bisa kokarin da al'ummomin kasashen duniya suka yi, an samu wasu ci gaba ta fuskokin tabbatar da ikon nakasassu da kafa wata al'umma maras shinge, amma har yanzu ba a iya tabbatar da ikon nakasassu ta fuskar samun guraban aikin yi da ilmi da kiwon lafiya kamar yadda ya kamata ba.
Mr. Zuma ya kara da cewa, dole ne gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta yi kokarin sa kaimi ga kamfanoni da su samar da guraban aikin yi da suke dacewa ga nakasassu, sannan hukumomin gwamnatin su yi namijin kokarin daukar karin ma'aikata nakasassu. (Sanusi Chen)