Ran 3 ga watan Disamba rana ce ta nakasassu ta duniya ta19 tun lokacin da aka fara wannan biki a shekara ta 1992. A 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta dauki tsauraran matakai domin ba da tabbaci ga hakkin nakasassu da kuma sa kaimi ga samar musu guraban aikin yi. A waje daya kuma, sassa daban daban na zamantakewar al'ummar Sin sun nuna kulawa ga nakasassu da kuma iyalansu, a kokarin kawar da bambancin da suke fuskanta, ta yadda za su yi zaman rayuwa cikin mutunci. To yanzu ga cikakken bayani.
Yang Jiaming, wani nakasasshe da ke yankin Panyu na birnin Guangzhou na kasar Sin ya samu aiki a shekara ta 2006 bayan da ya samu horaswa bisa taimakon da kungiyar kula da nakasassu ta wurin ta samar, a matsayinsa na edita na wani kamfanin tallace-tallace, yanzu yawan kudin da ya samu a ko wane wata yake kai kimanin Yuan 2000, sakamakon haka, an ba da tabbaci ga zaman rayuwarsa. Yang Jiaming ya gaya wa wakilinmu cewa, "shugaban kungiyar kula da nakasassu ta unguwarmu ya ba ni wata kwamfuta, wanda ya nuna goyon baya ga aikina. Daga baya kuma an gayara hanyar yadda ta dace da zaman rayuwata har gaban kofar dakina."