Babban daraktan wannan kamfani, mista Innocent Dimideclare Dimi a ranar Lahadi a yayin wata ganawa tare da manema labarai ya bayyana cewa, ya zama wajibi a ce kasar Congo tana da kasuwar hada hadar hannayen jari, duk da cewa kasar Congo karamar kasa ce, amma Allah ya yalwanta ta da arzikin ma'adinan kasa, haka kuma kasar na kan hanyar zama wata kasa mai karfin tattalin arziki.
Kamfanin hada hadar hannayen jari na "la financiere" zai fara ayyukansa gadan gadan a ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa a birnin Brazzaville, kamfanin nada hannun jari na biliyan guda wato kwatankwacin dalar Amurka miliyan biyu kuma zai tafiyar da aiki a karkashin wani kwamitin zartarwa. Kamfanin ne da ya hada masu hannayen jari daga kasashen Faransa, Congo da Cote d'Ivoire.
Mista Innocent ya kara da cewa, cibiyar kula da harkar kudi ta wannan kamfani za ta kasance a birnin Lille na kasar Faransa.
Kamfanin "la financiere" zai gudanar harkokin dama da suka shafi hada hadar hannayen jari kamar nazari a fuskar kudi, ajiyar kudi, dillanci, bincike kan harkar kudi, ajiyar takardun kudi, da dai sauransu.
Ita wannan cibiyar hada hadar hannayen jari ta kasance ta uku a cikin yankin CEMAC bayan ta kasashen Kamaru da Gabon.
Kuma hukumar raya tattalin arziki da cinikayya ta Afirka ta tsakiya CEMAC tana kunshe da kasashe shida da suka hada da kasashen Kamaru, Afrika ta Tsakiya, Congo, Gabon, Guinee-Equatoriale da Chadi.(Maman Ada)