Wadannan tsare tsaren ayyukan ukku, na farko ya kasance "kafa wani shafin internet na matasa" da Aristide Cyriaque Ndiele ya gabatar, tsarin "SIG" na Patrick Harry Bouetou Kadilamio da kuma tsarin "Yvon Sita" da ba'a bada sunan wanda ya gabatar da shi ba da ya janyo hankalin kamfanin VMK, wata kungiyar wannan taro da ta samar da wasu fasahohi ga kowane daga cikinsu.
Babban dandalin musanya tsakanin kasashen Afrika na da manufar karawa juna sani, yin amfani da sabbin kayayyakin harkokin sadarwa da fasaha, haka dandalin kasa da kasa ya taimaka wajen gabatar da kasidu daban daban game da sadarwa da suka hada da " Jaridu a kan internet a Afrika", "yunkurin samar da muhimman abubuwa duk da rashin hanya mai fa'ida ga tattalin arziki mai nagarta", "karshen zamanin wayoyin karkashin kasa na 'fibre optique'", da kuma "jaridun gargajiya a wannan zamani".
Dandalin kasa da kasa kan harkokin internet a nahiyar Afrika karo na biyu zai gudana a shekarar 2012 a babban birnin kasar ta Congo Brazzaville, a cewar masu shirya wannan taro. (Maman Ada)