Yara 'yan kasa da shakaru biyar miliyan 25 a Najeriya za su samu allurar rigakafin cutar shan inna
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kaddamar da wani gagarumin shirin yin wa yara 'yan kasa da shekaru biyar miliyan 25 a cikin kasar allurar rigakafin cutar shan inna, aikin da zai fara daga ranar 6 zuwa 9 ga watan Oktoba a cikin jihohi goma sha biyu dake arewacin Najeriya, in ji babban darektan cibiyar kasa ta bunkasa samar da ayyukan jiyya na farko, mista Ado Muhammad a ranar Jumma'a.
A cewarsa, wadannan yankuna na fuskantar barazanar yaduwar wannan cuta da suka kasance kashi 4 cikin 100 na fadin kasar Najeriya. (Maman Ada)