Ranar Lahadi 20 ga wata, kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta kaddamar da ayyukan yin rigakafin cutar shan-inna a kasar Somaliya da zummar tabbatar da burin yi wa kananan yara masu kasa da shekaru 5 a duniya kimanin miliyan 1.8 allurar rigakafin cutar a kasar .
A wannan rana, reshen Somaliya na kungiyar ya ba da sanarwa cewa, a cikin wadannan ayyuka na tsawon kwanaki uku, ma'aikatan kungiyar za su sake yin zagaye na biyu domin tabbatar da yi wa dukkan kananan yara allurar.(Amina)