Kwamitin tsaro na MDD ya yi kira ga daukacin kasashen duniya da su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin kare hakkokin yara a lokutan rigingimu ko yake-yake, tare da tabbatar da kare yara kanana daga fadawa halin cin zarafi, laifukan da kwamitin ya ce sun keta tabbatattun dokokin kasa da kasa.
Yayin zaman kwamitin na ranar Litinin 17 ga wata, an yi takarar irin nasarorin da aka cimma a wannan fanni, ko da yake a hannu guda, an bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da samun wadanda ke keta alfarmar yara ba tare da la'akari da dokokin da aka gindaya ba. Don gane da hakan ne ma kwamitin ya jaddada aniyarsa, ta daukar matakan da suka dace, wajen hukunta wanda duk aka kama yana keta alfarmar yara.
Har ila yau, kwamitin ya yi maraba da kudurin kara matsin lamba ga masu aikata wannan mummunan laifi, wanda sashen lura da yara yayin faruwar rigingimu na majalissar ke burin aiwatarwa. Daga nan sai kwamitin ya yi kira ga kasashe mambobin MDD, da su hada kai da ofisoshin majalissar na kasashensu, domin samarwa, tare da aiwatar da tsare-tsaren kare hakkokin yara yayin rigingimu ko yake-yake. (Saminu)