in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kan hanyar cimma yarjejeniya a cikin shawarwarin 'yan kasar Mali dake gudanarwa a Ouagadougou
2013-06-17 12:47:59 cri

Tawagar gwamnatin kasar Mali da gungun 'yan tawayen MNLA tare kuma da babban kwamitin hadin kan Azawad (HCA) za su iyar sanya hannu a ranar Litinin kan wata yarjejeniya a birnin Ouagadougou a karkashin shiga tsakanin shugaban kasar Burkina-Faso Blaise Compaore, a wani labarin da ya fito a ranar Lahadi da safe daga wasu majiyoyi masu tushe na wannan shiga tsakani.

Mai shiga tsakanin kungiyar ECOWAS, shugaban kasar Burkina-Faso Blaise Compaore, da sauran manyan jami'ai masu taimakawa wannan batu na wakilan kasa da kasa, sun yi aiki matuka a duk tsawon ranar Asabar bisa tsarin yarjejeniya. An ci gaba da wadannan ayyuka har zuwa da yamma, in ji wani jami'in diplomasiyya na kasar Burkina-Faso. Kuma jami'in ya shaida ma 'yan jaridar kasar Mali cewa, harkoki na gudanarwa yadda ake bukata, kuma suna samun cigaba yadda ya kamata.

Tun daga ranar 8 ga watan Junin da ya gabata, tawagar gwamnatin Mali a karkashin jagorancin mista Tiebile Drame, manzon musammun na shugaban kasar Mali, da aka baiwa nauyin tattaunawa tare da kungiyoyin 'yan tawaye masu makamai da kusoshin kwamitin hadin gwiwa na MNLA da HCA, suke shawarwari a birnin Ouagadougou. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China