Kawo yanzu, ko wane iyali kan sarrafa Zongzi a gida a farkon watan Mayu, nau'o'in Zongzi su ma sun karu. A arewacin kasar Sin, jama'a sun fi son Zongzi da aka sarrafa da busasshen dabino, amma a kudancin kasar Sin, jama'a sun fi son sanya garin jan wake, ko danyen nama ko gwaiduwan-kwan-agwagwa mai gishiri da sauransu.
Ban da wannan, a yayin bikin Duanwu, jama'a kan rataya irin ciyayin da ake kira "Ai" a kofar shiga gida, tare da tsaftace dakunansu. Irin ciyayin da ake ratayawa a kofar shiga gidan suna da kamshi na musamman, wanda ke iya korar sauro da kwari, haka kuma suna iya kau da cututtuka. Likitocin gargajiyar kasar Sin kan baiwa marasa lafiya su sha. Don haka ne, tun zamanin da, akan dauki bikin Duanwu a matsayin "bikin kiwon lafiya", a wannan rana, jama'a kan tsabtace daki, rataya ciyayin da ke maganin cututtuka, zuba ruwan da aka sa maganin gargajiyar kasar Sin a ciki, da kuma shan giyar da aka sa maganin gargajiyar kasar Sin a ciki. Duk wadannan al'adu suna nuna mana kyawawan al'adun al'ummar kasar Sin. (Lubabatu)