in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin gargajiya na Sinawa da ake kira Duanwu
2013-06-09 17:16:01 cri


Bikin Duanwu bikin gargajiya ne na Sinawa, wanda ke da dogon tarihi na tsawon shekaru kimanin dubu biyu. A kan yi wannan biki ne a ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ana kuma kiran bikin da sunaye iri iri, misali, bikin Duanyang, bikin watan Mayu, bikin mawaka, bikin wasan kwale-kwale da sauransu.

Game da asalin bikin, a bayanan da masana tarihi suka rubuta, an ce, bikin ya samo asali ne a zamani, da kuma al'adun kabilar Wuyue da ke kudancin kasar Sin, wadanda a lokacinsu, bikin ya kasance biki na ibada. Amma yanzu, an fi danganta bikin ne ga shahararen marubucin wake-waken nan mai suna Qu Yuan, wanda ya burge al'ummar kasar Sin sosai, ta yadda yake kishin kasarsa, da kuma wake-waken da ya rubuta, lamarin da ya sa jama'a suka fi kauna, da kuma yarda da ra'ayin da ya gabatar game da asalin bikin na Duanwu.

An haifi Qu Yuan a shekara ta 340 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, a birnin Danyang na kasar Chu, wato birnin Zigui na lardin Hubei na yanzu, kuma ya riga mu gidan gaskiya a shekara ta 278 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam.

Qu Yuan ya taba zama jami'i a masarautar daular Chu, kuma yana biyayya sosai ga sarkin daular, sai dai sauran jami'ai ba su sonsa, don haka bayan rasuwar sarkin, Qu Yuan ya yi gudun hijira, sakamakon kora da sabon sarkin kasar ya yi masa, bayan wasu mutane sun yada jita-jitar cewa wai ya ci zarafin sarkin, a karshe dai, Qu Yuan ya kashe kansa cikin kogin Miluo.

Qu Yuan, yana daya daga cikin manyan marubuta wake-wake a tarihin kasar Sin, kuma ya bullo da tsarin rubutu irin na "Chuci", mai dauke da salon al'adar gargajiya ta Sinawa ta nuna biyayya ga sarakuna..

Wani babban dalilin da ya sa al'ummar kasar Sin ke wannan biki na Duanwu shi ne, domin tunawa da marigayi Qu Yuan, da kuma irin ra'ayinsa na kishin kasa, kuma muna iya gano haka ne idan mun yi bincike a kan al'adu da dama da ake bi na yin bikin, ciki har da tseren kwalekwale, da cin wani nau'in abincin da ake kira Zongzi da sauransu.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China