Ban da wasan tseren kwale-kwale, cin Zongzi a bikin Duanwu wata al'ada ce ta daban ta jama'ar kasar Sin. Zongzi wani irin nau'in abinci ne da ake hadawa, ta hanyar kunshe shinkafa cikin ganye, wanda ke da dogon tarihi tare da nau'o'i da yawa. Amma ba wai an kirkiro Zongzi ne saboda tunawa da marigayi Qu Yuan ba ne, a'a, a game da asalinsa, in an yi bincike, za a tara ra'ayoyi da yawa. Akwai wani daga cikinsu da ya fi samun karbuwa, an ce, kafin shekaru dubu dari biyar, lokacin da aka fara yin amfani da wuta domin dafa abinci, a kan kunshe shinkafa da ganye a kuma kona shi a cikin wuta, bayan ya dafu sai a cire ganyen a ci, ko da yake, irin wannan abinci ba Zongzi ba ne, amma ana ganin shi ne asalin Zongzi. Amma a game da dalilin da ya sa al'ummar Sinawa ke cin Zongzi a yayin bikin Duanwu shi ne, domin an ce, bayan da Qu Yuan ya tsumduma cikin kogi, sai jama'a suka jefa Zongzi cikin kogi, domin fatan kifaye za su ci Zongzi a maimakon gawarsa.
Hanyar sarrafa Zongzi na bikin Duanwu
Abubuwan da ake bukata: Shinkafa da ganyen gora ko na ayaba, kuma da zare da wake da wasu dangin gyada.
1. Za a fara da sanya su cikin ruwa a jika su, amma a kwano daban-daban.
2 Bayan yini guda, a tsame shinkafar da koren waken daga cikin ruwa.
3. A wanke ganye, a fitar da su daga ruwa.
4. A lankwasa ganyen da za a sanya kayan abincin ciki.
5. A nade ganyen zuwa kusurwoyi.
6.A zuba shinkafa da koren wake da dangin gyada a ciki.
7.A kara sanya wani ganyen.
8.A kara sanya shinkafa, amma kada ya cika sosai.
9.A juya ganye domin a rufe shi sosai.
10. A rufe abubuwan da aka sanya a ciki da ganye da aka kara a baya, sannan a daure shi da zare.
11. Kamata ya yi, girmansa ya yi daidai da dunkulen hannu.
12. Idan lokacin dafa Zongzi ya yi, sai a zuba ruwa cikin tukuniya, in ya tafasa, sai a rage karfin wutar, a zuba shi a ciki bayan Zongzi ya dafu, sai a bar su cikin ruwan zafi har sai ruwan ya yi sanyi.
13.Daga nan sai a cire ganyen, a ci.