in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta bai wa Guinee-Bissau dalar Amurka miliyan 63 domin kawo gyaran fuska a fannin tsaro
2012-11-08 10:51:18 cri

Kungiyar tattalin arzikin yammacin kasashen Afrika (ECOWAS) ta bai wa kasar Guinee-Bissau dalar Amurka miliyan 63 domin shirinta na kawo gyaran fuska a bangaren tsaro da kariya, a cewar wata majiya mai tushe a ranar Laraba.

An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Laraba a Bissau tsakanin shugaban kwamitin kungiyar ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo da firaministan wucin gadi na kasar Guinee-Bissau, Rui Duarte de Barros.

Mista Ouedraogo ya bayyana a yayin bikin cewa, gyaran fuska a bangaren tsaron kasar Guinee-Bissau ya zama babban mataki mai muhimmanci domin kawo zaman lafiya a idon gamayyar kasa da kasa.

Idan ana son cimma ribar wannan shiri, to, ya kamata ya kasance a karkashin jagorancin al'ummar kasar Guinee-Bissau tare da taimakon kungiyar ECOWAS da kuma gamayyar kasa da kasa, in ji mista Ouedraogo tare da jaddada cewa, dole ne wannan gyaran fuska ya kasance bisa hanya guda tare da kawo gyaran fuska a fannin kundin tsarin mulki da na zabe.

A nasa bangare, firaministan Guinee-Bissau, ya yi kiran gamayyar kasa da kasa da ta bi sahun kungiyar ECOWAS.

Bayan sanar da shi a cikin watan Janairun shekarar 2012, shirin tura jami'an tsaro 1400 ritaya a cikin sojojin kasar ya samu jinkiri dalilin rashin kudi.

Rundunar sojojin kasar Guinee-Bissau na dauke da sojoji 11000, a cewar wasu alkaluma masu tushe, kuma gamayyar kasa da kasa take matsa lamba na ganin an rage wannan adadi zuwa sojoji 4000. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China