in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci da a maido da doka da oda a Guinea-Bissau
2012-12-14 10:01:22 cri

A ranar Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD, ya bukaci da a maido da cikakken doka da oda a kasar Guinea-Bissau, inda sojoji suka tunbuke gwamnatin a watan Afrilu.

Kwamitin sulhun ya bayyana rashin jin dadinsa matuka cikin wata sanarwar da ya bayar dangane da rashin ci gaba a kokarin da ake na maido da doka da oda a kasar da ke yammacin Afirka. Yana mai cewa, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kawai ta hanyar sasantawa, shirin mika mulki, hakikanin tattaunawa, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

A ranar 12 ga watan Afrilu ne, sojoji a Guinea Bissau suka yi juyin mulki a kasar da ta yi suna wajen juyin mulki, mummunan shugabanci da rikicin siyasa tun lokacin da kasar ta samu 'yanci daga kasar Portugal a shekara ta 1974.

Sojojin dai sun yi juyin mulki ne gabanin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka shirya gudanarwa a ranar 22 ga watan Afrilu.

Bugu da kari, sanarwar ta ce, kwamitin sulhun ya nuna damuwa matuka dangane da karuwar fataucin miyagun kwayoyi, tun lokacin da sojojin suka yi juyin mulki a kasar. Kwamitin ya kuma yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai sansanin mayakan sama na Bissalanca da ke Bissau a ranar 21 ga watan Oktoba, kana ya nuna damuwa matuka game da rahotannin kashe-kashe, keta hakkin bil-adama da ake aikatawa a kasar, inda ya bukaci da a gudanar da cikakken bincike kan wadannan al'amura.

Kwamitin sulhun ya kuma nanata muhimmancin kokarin kasa da kasa wajen warware rikicin Guinea-Bissau, ya kuma yi maraba da shawarar MDD, AU, ECOWAS da sauran hukumomin kasa da kasa na turo tawagoginsu zuwa Guinea-Bissau don kimmanta yanayin siyasa da tsaro a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China