A ganinsa, ya kamata, AU ta kafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasa da kasa. Yana mai cewa, ya zuwa yanzu, lokaci ya yi, da nahiyar Afrika ta nuna wa dukan fadin duniya karfinta na samar da dukiya. Tare da yin maraba da sauran kasashe da su zuba jari a nahiyar don sa kaimi ga samun moriyar juna. (Amina)