A lokacin taron, Jean Ping ya shedawa manema labarai cewa, dalilan dake jawo bunkasuwar tattalin arzikin Afrika cikin sauri ba sabo da kayayykin sayarwa kawai ba, kuma sabo da sha'anin da ba na ciniki ba, kamar su hidima da sadarwa, abin da ya nuna cewa, tattalin arzikin Afrika na kama hanyar samun bunkasuwa mai dorewa. Ya kara da cewa, bunkasuwar da kasar Habasha da Kenya suka samu na jawo hankalin kasa da kasa sosai duk da cewar rashin ci gaban da suka samu a sana'ar man fetur.