in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Sudan sun murkushe wani harin da 'yan tawaye suka kaiwa kudancin Kordofan
2013-05-06 10:00:51 cri

Sojojin gwamnatin kasar Sudan sun sanar da murkushe wani sabon harin da 'yan tawaye suka yi niyyar kaiwa a shiyyar Um Brimaita dake kudancin Kordofan, kamar yadda gidan radiyon kasar ta sanar a Lahadi, ranar 5 ga wata.

Kakakin Sojin kasar Al-Sawarmy Khalid Sa'ad ya fadi cewa, rundunar sojin kasar sun samu nasarar murkushe wani sabon harin da 'yan tawayen suka yi niyyar kaiwa a shiyyar Um Brimaita dake kudancin Kordofan, abin da ya jawo hasarar rayuka da dama ta bangaren 'yan tawayen, sannan kuma, in ji shi, sojojin sun samu nasarar kwace makamai da na'urori da dama tare da raunata wassu 'yan tawayen.

Sojojin gwamnatin Sudan din sun samu damar kakkabe duk wassu 'yan tawaye daka iya fakewa a wannan wuri har zuwa wassu 'yan kwanaki, in ji shi, yana mai bayanin cewa, niyyar 'yan tawayen ita ce su lalata wassu ababen more rayuwa a wajen.

A makon da ya gabata ne, sojojin gwamnatin na Sudan suka sanar da murkushe wani shigen harin da 'yan tawayen suka yi niyyar kaiwa a unguwar Um Rawaba da kuma Alla Kareem duka a kudancin Kordofan, yana mai bayanin cewa, 'yan tawayen sun lalata babbar hasumiyar sadarwa da kuma tashar samar da wutan lantarki, sannan suka sace kayayyakin al'umma mazauna wajen.

Jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile dai suna fuskantar arangama tsakanin 'yan tawaye na SPLM da sojojin gwamnati tun shekarar 2011 bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kanta.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China