in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai tsohon shugaban Masar asibitin soji sakamakon tabarbarewar lafiyarsa
2012-12-28 10:45:49 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA ya ruwaito wata kafar tsaron kasar tana cewa, an mayar da tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak zuwa wani asibitin soja mafi kusa da ke birnin Alkahira daga asibitin gidan yarin Tora sakamakon tabarbarewar lafiyarsa.

Tun a ranar Alhamis ne babban mai shigar da kara na kasar Talaat Ibrahim Abdullah ya bayar da umarni a mayar da Mubarak din asibitin soja, sannan a dawo da shi da zarar ya murmure ba tare da wani bata lokaci ba.

A makon da ya gabata ne aka mayar da Mubarak asibitin soja na Maadi daga asibitin gidan yarin da ya ke tsare domin a yi masa wasu gwaje-gwaje daga bisani kuma aka dawo da shi.

A baya-bayan nan, tsohon shugaban wanda ke fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai sakamakon umarnin da ya bayar na kashe masu bore a shekara ta 2011, ya samu rauni a kansa bayan ya fadi a bayan gidan yarin da ake tsare da shi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China