in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Libya sun gaskanta labarin mutuwar Gaddafi
2011-10-21 14:11:58 cri

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, dakarun adawa sun murkushe mulkin Gaddafi a ranar 23 ga watan Agusta na bana wato bayan da ya rike mulki a kasar Libya har na tsawon shekarun 42. Yanzu dai, labarin mutuwarsa shi ma ya alamanta cewa, an kawo karshen zamanin mulkin Gaddafi a kasar Libya a hukunce. A yayin taron watsa labaran da aka yi a wannan rana, shugaban kwamitin zartaswa na kwamitin wucin gadin duk kasar Libya Mahmud Jabril ya nuna cewa, ya kamata jama'ar Libya su gano cewa, yanzu, lokaci ya yi da su kafa wata sabuwar kasa a Libya wato kasar Libya mai hadin kai tare da kabila daya da makoma daya. Jabril shi ma ya bayyana cewa, shugaban kwamitin wucin gadin Mustafa Abdel Jalil zai sanar da labarin 'yantar da duk kasar Libya a ranar 22 ga wata, kuma zai yi cikakken bayani labaran da suka shafi mutuwar Gaddafi.

Amma, masu lura da al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, a hakika dai, an riga an gano sakamakon halin siyasa da Libya ke ciki kafin wata guda, yanzu dai, Gaddafi ya mutu, sabane-sabane dake cikin sabon mulkin Libya za su fito a kai a kai, ko shakka babu, hakan zai kawo barazana ga hadin kai na sabon mulkin kasa da zaman karko na zamantakewar al'ummar kasar Libya. Shi ya sa, dole ne jama'ar Libya su yi kokari domin tabbatar da makoma mai kyau.(Jamila)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China