in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Libya sun gaskanta labarin mutuwar Gaddafi
2011-10-21 14:11:58 cri

A ranar 20 ga wata, halin siyasa da kasar Libya ke ciki ya yi manyan sauye-sauye, a wannan rana, dakarun mahukuntan kasar sun mamaye birnin Sirte wato garin Gaddafi, kuma, mahukuntan Libya sun gaskanta cewa, sun kama Gaddafi, daga baya, ya mutu a sanadin rauni mai tsanani. Masu lura da al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, mutuwar Gaddafi tana da babbar ma'ana saboda ta alamanta cewa, an riga an kawo karshen wani zamani a kasar Libya.

A ranar 20 ga wata da safe, da misalin karfe 8, agogon kasar Libya, dakarun mahukuntan kasar sun fara faramaki ga sansanin soja na karshe dake birnin Sirte inda sojojin dake karkashin jagorancin Gaddafi ke sauka, bayan minti wajen casa'in, sojojin Gaddafi sun daina nuna kiyayya, bi da bi ne kowanensu ya gudu. Sai nan take dakarun mahukuntan kasar sun yi sumaye a wannan yanki. Bayan da mahukuntan Libya suka sanar da labarin mamaye Sirte, ba da dadewa ba, sun nuna cewa, sun kama Gaddafi. Wani jami'in hukumar rike mulkin kasar ya bayyana cewa, a wannan rana da asuba, motocin Gaddafi sun gamu da harin da kungiyar tsaro ta NATO ta yi musu yayin da suke kan hanyar tsere, daga baya, an kama Gaddafi a wurin dake dab da Sirte. Amma, ba da dadewa ba, a birnin Benghazi dake gabashin kasar, kakakin kwamitin wucin gadin duk kasa na kasar Libya Abdel Hafez Ghoga ya sanar da cewa, an kama Gaddafi ne a yayin yakin da aka yi a Sirte a wannan rana, kuma ya mutu a sanadin rauni mai tsanani da ya ji.

Ban da wannan kuma, wani kwamandan aikin soja na mahukuntan Libya ya nuna cewa, 'dan Gaddafi na hudu Mutassem Gaddafi da ministan tsaron kasa na Gaddafi sun mutu a Sirte a ran nan. Kuma an kama kakakin mulkin Gaddafi Mussa Ibrahim a wurin dake kusa da Sirte.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China