in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Libya sun gaskanta labarin mutuwar Gaddafi
2011-10-21 14:11:58 cri

Bayan da aka samun labarin mutuwar Gaddafi, sojoji da yawa na mahukuntan Libya sun yi yawo a tituna domin taya murna, wasu sun harba bingigogin sama domin nuna farin ciki sosai da suke ciki. A Tripoli, mazaunan birnin sun fito daga gidaje sun yi yawo a tinuna, a sanadin haka, an samu cunkuso mai tsanani a birnin. Wasu mutane sun bai wa mutanen dake cikin motoci kyautar alewa domin taya murna tare. A Bani Walid da Benghazi, mutane su ma sun yi aikin taya murna kamar yadda mutanen dake sauran wuraren kasar ke yi. Amma, labarin mutuwar Gaddafi bai rage damuwar jama'ar Libya kan makomarsu a nan gaba ba. Wasu sun bayyana cewa, mutuwar Gaddafi ba ta iya nuna cewa, halin da Libya ke ciki zai samu kyautatuwa yadda ya kamata ba, yaki ya rushe gidajensu, suna fatan za su iya yin rayuwa cikin zaman lafiya bayan yaki.

Bayan da bangaren Libya ya sanar da labarin mutuwar Gaddafi a ranar 20 ga wata, da sauri, kasa da kasa da wasu kungiyoyin kasashen duniya kamarsu Amurka da Faransa da Jamus da kungiyar kasashen Larabawa sun nuna ra'ayoyinsu kan wannan batu inda suka bayyana cewa, suna fatan mahukuntan kasar Libya za su kafa ikon mulkin kasa irin na dimokuradiya a kasar. Shugaban kasar Amurka Obama ya yi jawabi a fadarsa inda ya nuna cewa, bangaren Amurka yana fatan za a kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Libya tun da wur wuri kuma za a tabbatar da dimokuradiya da kuma shirya babban zabe bisa adalci a kasar cikin lokaci.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China