in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar rike mulkin kasar Libya ta nuna cewa, an riga an tabbatar da wurin buyan Gaddafi
2011-09-29 14:44:44 cri

A daidai wannan lokaci, wato kafin za a kammala yakin Libya, zamantakewar al'ummar kasa da kasa suna cikin zulumi kan yaduwar makaman guba masu sa cuta a kasar. Kwanan baya, wani babban jami'in majalisar dinkin duniya ya nuna a yayin taron kwamitin sulhu cewa, dole ne a sarrafa dakunan ajiye makamai na kasar Libya, in ba haka ba, kila 'yan ta'addanci za su yi amfani da shi. Kafin wannan lokaci kuma, wasu kasashen Afirka kamarsu Nijer da Nijeriya sun taba nuna damuwarsu kan makaman da abin ya shafa, wato kila kungiyar "Algaida" a wurin za su same su. Dakarun hukumar rike mulkin Libya sun gano dakunan ajiye makamai na siri na Gaddafi da yawa yayin da suka yi yaki. Kuma da zarar an gano, sai an kwace dukkan makamai nan take. Kazalika, a kudu da kuma tsakiyar kasar Libya, an gano wasu makaman guba masu sa cuta da kayayyakin kera makaman nukiliya, shi ya sa, zamantakewar al'ummar kasa da kasa suna yin damuwa da zaman lafiyar wadannan makamai.

Kafin wannan lokaci, shugaban kwamitin wucin gadin kasar Libya Mustafa Abdel Jalil ya taba bayyana cewa, a halin yanzu, wadannan makamai suna karkashin sarrafawar hukumar rike mulkin kasar, kuma ya bukaci masanan da abin ya shafa da zamantakewar al'ummar kasa da kasa da su dauki matakai masu dacewa da su rushe wadannan makaman guba masu sa cuta da kayayyakin kera makaman nukiliya cikin lumana.(Jamila)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China