in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar rike mulkin kasar Libya ta nuna cewa, an riga an tabbatar da wurin buyan Gaddafi
2011-09-29 14:44:44 cri

Saboda dakarun hukumar rike mulkin kasar Libya sun gamu da kiyayya mai karfi daga wajen masu goyon bayan Gaddafi, shi ya sa, a ranar 28 ga wata, suka sha wahala yayin da suke kai hari ga garuruwa biyu na karshe dake karkashin mamayen Gaddafi, a sanadin haka, dakarun hukumar kasar Libya sun bukaci kungiyar tsaro ta NATO da ta kara karfin kai hari ga masu goyon bayan Gaddafi daga sama. A sa'i daya kuma, hukumar ta nuna cewa, an riga an gano wurin buya na Gaddafi da yaransa biyu.

A halin yanzu, dakarun hukumar rike mulkin Libya da masu goyon bayan Gaddafi suna yin kazamin yaki a garuruwa biyu wato Sirte tsohon garin Gaddafi da Bani Walid dake da nisan kilomita 170 daga Tripoli, babban birnin kasar, sojoji masu goyon bayan Gaddafi sun nuna kiyayya mai karfi gare su. Game da wannan, wani kwamandan dakarun hukumar Libya Walid Khaimej ya bayyana cewa, sun gamu da harin da aka kai musu da makamai masu linzami da igogi, shi ya sa, sojojin rundunarsu sun riga sun daina dosa gaba zuwa wurin yaki, suna jiran sojojin da za su zo daga Tripoli da Zawiyah. Mhaimej ya kara da cewa, koda yake kungiyar NATO tana kai hari ga masu goyon bayan Gaddafi daga sama, amma ba ta yi iyakacin kokari ba wato bai biyan bukatunsu ba, ya bukaci kungiyar NATO da ta kara karfin kai hari ga masu goyon bayan Gaddafi daga sama. An sami labari cewa, babban kwamandan a wurin yaki na Bani Walid Daw Saleheen ya riga ya rasa rai a sanadin harben harsashin roka da masu goyon bayan Gaddafi suka yi masa a ranar 28 ga wata.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China