in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar rike mulkin kasar Libya ta nuna cewa, an riga an tabbatar da wurin buyan Gaddafi
2011-09-29 14:44:44 cri

A ranar 27 ga wata, babban jami'in aiki soja na hukumar rike mulkin kasar Libya Hisham Buhagiar ya gaya wa manema labarai cewa, an riga an tabbatar da wurin buya na Gaddafi, yanzu, Gaddafi yana boye a yankin Ghadamis dake yammacin kasar Libya wato kusa da iyakar yankin kasar Aljeriya, yana karkashin tsaron kabilar wurin wato 'yan kabilar Tuareg na wurin suna goyon bayansa cikin dogon lakaci. Hukumar rike mulkin Libya tana yin shawarwari da su. Wani kakakin bangaren soja na hukumar Libya Abdel-Rahman Busin ya bayyana a ranar 28 ga wata cewa, kila Gaddafi yana boye a hamadan kudancin kasar Libya dake kusa da iyakar yankin kasa ta Aljeriya. Wannan yanki ya yi girma sosai, shi ya sa, da kyar hukumar ta sarrafa shi, ban da wannan kuma, Gaddafi zai kaura daga wani wuri zuwa wani wuri daban cikin sauri. Kakaki daban na bangaren soja na hukumar rike mulkin Libya Ahmed Bani shi ma ya bayyana a wannan rana cewa, a halin yanzu, ba a iya gaskanta da wannan labarin dake alakar sawon Gaddafi ba, saboda haka, hukumar za ta fara aikin kama shi bayan da ta mamaye duk daukacin yankin kasar Libya. Amma a sa'i daya kuma, Bani ya nuna cewa, hukumar ta riga ta gano wuraren boye na yaran Gaddafi biyu. Dansa na biyu Seif al-Islam yana boye a Bani Walid, daya dan nasa Mutassem Gaddafi yana boye a Sirte.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China