in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake jinkirtar da lokacin kafuwar sabuwar gwamnatin kasar Libya
2011-09-28 15:02:29 cri

A 'yan kwanakin nan, mahukuntan kasar Libya tana yin shawarwari tare da bangarori daban daban kan kafuwar sabuwar gwamnatin kasar. Tun bayan da aka hambarar da Kanar Gadhafi a watan jiya, mahukuntan kasar Libya NTC ya bada tabbaci a ran 11 ga watan satumba cewar zai kafa gwamnatin wucin gadi, a cikin mako guda ko kwanaki 10. Amma bayan mako guda, kwamitin NTC ya sake taken da labarin cewa, ba a cimma daidaito kan kafuwar sabuwar gwamnati ba. A ran 20 ga wata, Mahmud Jibril, shugaban kwamitin zartaswa na NTC ya ce, watakila za a kafa sabuwar gwamnatin kasar Libya a cikin kwanaki goma masu zuwa. Amma an yi hasashen cewa, manyan kusoshin kwamitin NTC ba su samu daidaito ba kan wasu sabbin mukaman ministoci, saboda haka ana ci gaba da tattaunawa kan batun. A ran 27 ga wata kuma, Mustafa el-Huni, wani mamba na kwamitin NTC ya nuna cewa, bayan kammala shawarwari tare da bangarori daban daban, kwamitin ya tsai da kudurin jinkirtar da lokacin kafuwar sabuwar gwamnatin, har sai an 'yantar da duk kasar Libya daga magoyan bayan Gadhafi.(Kande Gao)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China