A ran 27 ga wata, dakarun mahukuntan kasar Libya sun ci gaba da gwabzawa da magoya bayan Gadhafi a garin Sirte.daya daga cikin dakarun mahukuntan mai suna Fateh Marimri ya ambata cewa, yanzu mahukuntan kasar na yin musayar wuta da magoya bayan Gadhafi a wurin da ke kusa da otel din Mahari da ke garin. Magoya bayan Gadhafi sanye da tufafin fararen hula sun bude wuta ga dakarun mahukuntan kasar da manyan makamai. Domin kiyaye mutuwa da raunana jama'a, dakarun mahukuntan kasar sun ki yin amfani da irin wadannan makamai. Marimri ya kara da cewa, yanzu daya daga cikin'ya'yan Gadhafi yana garin Sirte, wanda yake samun kariya daga magoya bayansa sosai. Ban da wannan kuma wani daga cikin dakarun mahukuntan kasar Libya mai suna Ali Zaidi ya bayyana cewa, yanzu dakarun sun yi gaba zuwa cibiyar garin, kuma ana sa ran karawa da juna nan ba da jimawa ba. A wannan rana da safe, dakarun sun sanar da mamaye tasoshin jiragen ruwa na garin Sirte, kuma zasu nufi zuwa cibiyar garin. Kazalika dakarun sun ce, sun gano dimbin makamai a cikin gidajen mazauna garin. A garin Bani Walid, sakamakon gamuwa da dagiya daga magoya bayan Gadhafi, dakarun mahukuntan kasar sun janye jiki daga wasu yankunan da suka taba mallakarsu.