Ban da manufofinsa ta fuskar tattalin arziki, masu binciken al'amuran duniya na kasar Zambia sun sanya ayar tambaya kan yadda gwamnatin Sata za ta iya kula da ra'ayin bainar jama'a, inda suka ce, yadda ake kokarin kayyade kafofin watsa labaru, da magance samar wa jama'a bayanai, ba za su amfana wajen daukaka matsayin kasar Zambia a idanun mutanen duniya ba.
Bugu da kari, an ce, dole ne shugaba Sata ya yi kokarin cika alkawarinsa na kau da matsalar Barotseland, batun da ya shafi yadda kungiyar 'yan aware ta ''yantar da Barotseland' ta yi gangami a yankin Mongu da ke yammacin kasar, inda ta ta da tarzoma da dauki ba dadi da 'yan sanda.
Mista Sata ya taba zama minista a gwamnatin kasar Zambia karo da dama, kana ya yi suna saboda yadda yake son daukar mataki mai tsanani. Sai dai an ce kara nuna sassauci zai taimaka wajen neman samun amincewa daga jama'ar kasar. (Bello Wang)