Michael Sata da jam'iyyarsa ta kungiyar masu kishin kasa (PF) sun yi nasara a babban zaben kasar Zambia a wannan karo, ta yadda suka kawo karshen mulkin da jam'iyyar hada kan jam'iyyu masu bin ra'ayin dimokuradiyya (MMD) ta kwashe shekaru 20 tana ta gudanarwa, irin sauyawar yanayi da ta janyo hankalin bangarori daban daban na duniya zuwa wannan kasar mai yawan al'umma na fiye da miliyan 10 da ke kudancin nahiyar Afirka.
Bayan da Michael Sata ya ci zaben, ya sheda wa manema labaru cewa, ya fahimci kalubaloli da ke gabansa, inda ya ce, 'Hakan ta sa tamkar an kama wata hanyar cin nisan zango, inda za a gamu da matsaloli da yawa.'