in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Zambia na fuskantar kalubaloli daban daban
2011-09-26 16:37:11 cri

A lokacin da ya fara yakin neman zabe, Michael Sata ya yi alkawarin kawo babban sauyin yanayi ga kasar Zambia cikin kwanaki 90 bayan da ya hau kan kujerar mulki, amma har zuwa ranar 23 da yamma lokacin da ya yi jawabin fara aiki a gaban dubun dubatar masu goyon bayansa, Sata ya kasa bayyana wani cikakken shiri kan yadda zai yi kokarin cika alkawarin. Sai dai ya sake nanata cewa, gwamnatinsa za ta mai da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa, da kula da mazauna yankin iyakar kasa, gami da kokarin rage gibin da ke tsakanin masu kudi da marasa galihu.

Zambia ta kasance daya daga cikin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, inda kashi 70% na al'ummar kasar ya kasance na masu fama da talauci. Masu bincike kan al'amuran duniya na ganin cewa, yawancin masu goyon bayan Michael Sata direbobi me masu tuka bas, 'yan talla a kasuwa, da jama'a marasa ayyukan yi, don haka suna Allah-Allah wajen ganin Mista Sata ya iya samar da karin guraben aikin yi, da kara albashin ma'aikata. Amma wadannan mutane ba su da wayewa sosai, kana cikin sauki ana iya hure musu kunne, don haka idan aka gaza biyan bukatarsu, to, mai yiwuwa ne za su ta da zaune tsaye a kasar, abin da ya riga ya janyo damuwa daga sassa daban daban na kasar Zambia.

Ban da haka kuma akwai wasu manufofin da Mista Sata bai tabbatar da su ba tukuna, ga misali, ya taba zargin kamfanonin waje da kwashe ma'adinan kasar Zambia, wadanda ba su samar da moriya ga kasar. Zuwa karshen yakinsa na neman zabe, Mista Sata ya sheda wa manema labaru cewa, ba zai yarda da kamfanonin waje su ci kare babu babbaka da bata albarkatun kasar Zambia ba. Sai dai kafin a sanar da sakamakon babban zaben kasar, Mista Sata ya bayyana cewa, idan ya zama shugaban kasa, ba zai kara karbar haraji daga kamfanoni masu hakar ma'aninai don kara kudin shiga na gwamnati ba. Kana cikin jawabin fara mulki da ya yi a ranar 23 ga wata, Mista Sata ya ce kasarsa za ta ci gaba da hadin gwiwa da masu zuba jari na waje, kana yana maraba da karin kamfanoni da su saka jari a fannin hakar ma'adinai a kasar, sai dai ya bukaci masu zuba jari da su bi dokoki na kare hakkin kwadago.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China