Gaba daya, wakilai mahalartan taron da suka zo daga kasashen Afirka sun bayyana cewa, suna fatan gwamnatin kasar Sin za ta samar musu sakamakon rage abkuwar bala'in da ta samu, ta yadda kasashen Afirka za su daga matsayinsu na yaki da bala'in fari. Ministan kula da harkokin ba da agaji ga bala'i da 'yan gudun hijira na kasar Uganda Stephen Oscar Mallinga ya nuna cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bala'in fari ya kan faru a kasar Uganda, kusan sau daya a duk shekaru hudu ko biyar, musamman ma a yankin arewa maso gabas da yankin yamma na kasar. A sabili da haka, wadannan wurare suna fama da rikicin karancin abinci mai tsanani saboda fari. Gwamnatin kasar Uganda ta mai da hankali sosai kan wannan taro saboda ta sa rai cewa, za ta koyi sakamakon da kasar Sin ta samu kan wannan fanni."
Game da wannan, minsita Li Liguo ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana son yin kokari tare da jama'ar kasashen Afirka domin kara karfafa hadin gwiwa da cudanya kan batun magance da kuma yaki da bala'in fari tsakaninsu. Li Liguo ya ce, "Nan gaba, kasar Sin za ta kara karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afrika wajen rage abkuwar bala'in fari da kuma ba da agaji ga jama'ar dake fama da bala'in. Kasar Sin tana son samar musu taimako kan wannan fanni, kuma tana son yin nazarin da abin ya shafa tare da kasashen Afirka domin samar musu goyon bayan fasahar yaki da bala'in fari."
Ban da wannan kuma, Li Liguo ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kafa wani tsari na hadin gwiwa tare da kasashe da kuniyoyin da abin ya shafa domin rage abkuwar bala'in fari a duk duniya, musamman ma a nahiyar Afirka.(Jamila)