A yayin taron, ministan harkokin jama'ar kasar Sin Li Liguo ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta samar da taimakon abinci cikin gaggawa ga kasashen Afirka dake fama da bala'in ta hanyoyi daban daban. Ya ce, "Yanzu, wasu kasashen Afirka suna fama da bala'in fari mai tsanani da karancin abinci mai tsanani, a sanadin haka, gwamnatin kasar Sin ta tsai da cewa, za ta samar da taimakon abinci mai darajar kudin Renminbi yuan miliyan 533 da dubu 200 domin taimakawa kasashe masu fama da bala'in. Ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta samar da taimakon abinci ba, har ma ta gabatar da kudin musaya domin sayen abinci."
Li Liguo ya ci gaba da cewa, yanzu, gwamantin kasar Sin tana kokarin cika alkawarinta, kuma, a farkon wannan wata, an riga an fara jigilar da taimakon abinci ga kasashen Afirka dake fama da bala'in, nan gaba, za a ci gaba da gudanar da wannan aiki yadda ya kamata.