Shugaban hukumar darektocin kamfanin GCDGL Kwame Akuffo ya ba da sanarwar cewa, daga mako mai zuwa, kamfanin zai dauki ma'aikata 2500 don ya fara gudanar da ayyukansa, amma zai dauki ma'aikata 50,000 ne cikin dogon lokaci.
Har ila yau, ya yi alkawarin cewa, kamfanin zai gudanar da ayyukansa ba tare da gurbata muhalli ba ta yadda zai bar kyakkyawan tarihi ga na baya.
Bayanan da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu sun yi nuni da cewa, kamfanin GCDL mallakin Zoomlion Ghana, kamfani ne da ke kan gaba a harkar kula da muhalli a kasar, ya amince ya biya gwamnatin kasar dala miliyan 17, amma ya zuwa yanzu ya biya dala miliyan 1.7 ne kwatankwacin kashi 10 cikin 100 ke nan na adadin kudin. (Ibrahim)