A halin yanzu dai masu sabon kamfanin sun yi alkawarin samar da guraben aikin yi 50,000 cikin dogon lokaci. Kuma alkaluman kididdiga a hukumance sun nuna cewa, tsakanin shekarun 1960 zuwa 1980 kamfanin na GCD ya samar da sama da karati miliyan 2.5 na Lu'u-Lu'u a shekara.
Ko da yake adadin ya ragu zuwa 157,000 a shekarar 2003 kana ya ci gaba da raguwa har zuwa kasa da 79,000 a shekarar 2007. Kuma an dangantaka al'amarin ga rashin saka jari, wanda ya haddasa tabarbarewar harkar hakar ma'adinai.
Har ila yau Mahama ya yi alkawarin cewa, gwamnatin za ta ci gaba da ayyukan hako ma'adinai, don hako sauran albarkatun da Allah ya hore wa kasar.
A jawabinsa mataimakin ministan filaye da albarkatun kasa Henry Ford Kamel ya bayyana cewa, durkushewar kamfanin na GCD ya dakushe fata da tunanin al'ummomin Akwatia.
Ya ce, dan haka gwamnatin za ta baiwa sabon mai zuba jarin goyon baya ta kowa ce fuska ta yadda zai cika alkawarun da ya yiwa jama'a.