Hakazalika, jaridar New York Times ta kasar Amurka ta bayar da wani rahoto a ran 16 ga wata, cewar yanzu gwamnatin kasar Amurka tana kokarin neman damar korar Gaddafi daga kasar Libya, wato tana neman wata kasa wadda za ta iya karbar Gaddafi. Wani jami'in kasar Amurka ya ce, "kasashen da za a iya zaba kalilan ne." Jaridar New York Times ta kiyasta cewa, mai yiyuwa ne wata kasar Afirka za ta iya karbar Gaddafi.
Game da wannan rahoton da jaridar New York Times ta bayar, manazarta sun nuna cewa, idan wannan labari ya kasance na gaskiya, to wannan na alamta cewa, kasar Amurka tana kokarin koyon darussa daga yakin Iraki, wato tana kokarin neman kungiyoyin siyasa na kasar Libya da su canja gwamnatinsu da kansu, amma ba bisa matakin soja kawai ba. Idan an iya korar Omar Mouammer al Gaddafi daga mukaminsa ta hanyar zaman lafiya, a kalla kasar Amurka za ta iya rage yawan kudin da take kebewa aikin soja.
Amma, har yanzu malam Omar Mouammer al Gaddafi na nuna adawa da irin wannan shiri na kasar Amurka. A kwanan baya, har sau da dama ne 'ya'yansa suka bayyana cewa Gaddafi ba zai sauka daga mukaminsa ba, kuma ba zai bar kasar Libya ba. (Sanusi Chen)